Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Ofishin hulɗar jama'anta Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci a cikin wata sanarwa ta bayyana: Mintuna kaɗan da suka wuce ta kakkabo wani jirgi maras matuƙi na zamani MQ1 ta hanyar an anfani da sabuwar na’urar kariyar sama ta zamani ta rundunar sararin samaniya ta Rundunar Kare Juyin Juya Hali kuma ƙarƙashin ikon cibiyar sadarwar haɗin gwiwar kariya sama ta ƙasar a sararin samaniyar mashigar Hormuz.
A cikin yaƙin da aka tilasta na uku, an harbo ɗaruruwan jiragen mara matuƙa na makiya ta hanyar kariyar sama ta ƙasar Iran waɗanda jiragen "Lucas", "Hermes", "MQ-1" da "MQ-9" ma suna cikinsu.
Haka kuma a baya hulɗar jama'a ta Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta ba da labarin lalata wani jirgin ruwa maras matuƙi (shahpad) na sojojin Amurka a mashigar Hormuz. An gudanar da wannan aiki da safiyar yau Talata.
…………..
Ra'ayinka